Type Here to Get Search Results !

Main event

Mukaddashin CJN Ya rantsar Da Manbobin Kwamitin Sauraron Kararrakin Zabe 250


Legit Hausa

Ibrahim Tanko Muhammed, sabon mukaddashin shugaban alkalan Najeriya (CJN) a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe su 250, gidan talbijin din Channels TV ta ruwaito.

A lokacin bikin kaddamarwar da ya gudana a Abuja a ranar Asabar, Muhammed ya bukaci mambobin kwamitin sauraron kararrakin zaben da su gudanar da ayyukansu cikin mutunci da tsoron Allah a zukatansu. Da farko, Legit.ng ta rahoto sabbin bayanai da suka billo kan dalilin da yasa gwamnatin tarayya ba ta jira kotu ta bayar da umurni akan tsige babban alkalin-alkalan Najeriya Walter Onnoghen ba a Abuja a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu.

An sanya ran cewa Justice Onnoghen zai kaddamar da kwamitocin alkalai 250 da za su jagoranci gudanarwar zabe mai zuwa. Majiyar tace: “Adadin mambobin da za su zauna a kwamitocin zabe su 250 ne. Kwamitocin sun hada da na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki, kotun sauraron kararrakin zaben gwamna, da kuma na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki na jiha.

“Cire shi da aka yi cikin gaggawa don kokarin dakatar da taron ne ko kuma yunkurin cire sunayen wasu alkalai daga jerin sunayen. Hakan ce za ta kasance."
 


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies