Marubuciya Littafan Addinin Musulunci Aisha Lemu Ta Rasu


Legit Hausa
Allah ya yiwa shahararriyar malama, marubuciyyar littafan addinin musulunci kuma wadda ta kafa kungiyar mata musulmi na tarayya, FOMWAN, Aisha Lemu rasuwa. Aisha Lemu ta rasu tana da shekaru 79 a duniya.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Lemu ta rasu ne a yau Asabar a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Direkta Janar na hukumar NITDA, Sheikh Isa Pantami shima ya tabbatar da rasuwarta inda ya yi addua'ar Allah ya gafarta ma ta. Marigayiyar mata ce ga Sheikh Ahmad Lemu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post