Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa a kan halayen
wasu 'yan Najeriya da ke amfani da kabilanci ko addini domin aikata zalunci da
aikata rashawa inda ya ce yaudara ce da shirme. A jawabin da ya yi a wurin
taron cin abinci na musamman inda ya gayyaci tsaffin abokan aikinsa yayin da ya
ke mulkin soja (tsakanin 1984-1985) da aka gudanar a ranar Lahadi a fadar Aso
Rock, shugaban kasar ya ce rashawa ce ke sanya wasu boyewa cikin rigar addini
da kabilanci.
Domin kafa hujja a kan abinda ya fadi, shugaban kasar ya
bayar da labarin gwagwarmayar da sha a kotun zabe a shekarun 2003, 2007 da 2011
inda 'yan uwansa musulmi 'yan arewa ne suka kayar da shi yayin da Kiristoci
daga kudu ke kare shi. Ga wani sashi cikin jawabinsa: "Wasu dalilai sun
sanya ni magana a kan wani da nake matukar mutuntawa a Najeriya.
A 2003 da na fara, ana fara shigar da karar zaben shugaban
kasa ne daga kotun daukaka kara. A lokacin shugaban kotun ajin mu daya da shi a
makarantar sakandire, ni da shi da Shehu Musa Yaradua duk ajin mu daya. Lauya
na a wannan lokacin, Mike Ahamba kirista ne kuma Ibo. Zuwa na kotu ranar farko,
Ahamba ya ce min yana bukatar jerin sunayen wadanda su kayi rajistan zabe a
wasu yankuna domin ya nuna cewa kuri'un da aka samu a wuraren na bogi ne.
Ya bukaci su rubuta bukatarsa kuma su rattaba hannu, kuma su
kayi hakan. "A yayin da suka zo yanke hukunci, sai suka ki ambaton zancen.
A cikin jerin alkalan wani Kirista kuma dan kabilar Ibo ne ya daga hannunsa ya
tunatar da su abinda lauya na nema. Shin mun nemi a bamu rajistan wadanda su
kayi zabe a wadannan yankunan? Idan ba muyi ba kuma menene dalili? Nan suka yi
masa taron dangi suka ce ya yi shiri. Hakan yasa ya rubuta hukuncinsa daban da
nasu.
A yau shine jakadar Najeriya a Amurka. "Na shigar da
kara a kotun koli. Wanene babban alkalin kotun? Musulmi ne Fulani daga Zaria.
Bayan watanni 27, mun sake komawa kotun. Ahamba ya yi bayani na sa'o'i 2 da
mintuna 45 amma suka ce masa za su tafi hutu a goben ranar. Sunyi hutu na
watanni 3 kuma da suka dawo hutun su kayi watsi da shar'ar namu cikin mintuna
45.
"A 2007, abinda ya sake faruwa kenan. Wanenen Alkalin
Alkalai? Musulmi ne dan Arewa kuma bayan watanni 18 su kayi watsi da shar'ar.
"A karo na 3 a 2011, Alkalin alkalai shima musulmi ne, Fulani daga jihar
Jigawa. Bayan watanni 8 ya yi watsi da shar'iar. Saboda haka batun amfani da
kabilanci da addini a Najeriya wurin cimma wasu manufofi rashawa ne
tsantsagwaronta. Duk ida muka samu kanmu, muji tsoron Allah mu tsare imanin
mu."
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi