Bisa wannan dalili ne Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi tare da rakiyar tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari, da Mataimakinsa K. Aliyu da sauran hadiman Gwamna Bagudu, suka kai ziyarar bazata na gani da ido yadda aikin hada wajen taron ke tafiya. Gwamna Bagudu ya isa filin wasa na Haliru Abdu da misalin karfe 5;17 na yamma.
Ga dukkan lamu a cikin darae ne za a hada rumfa da za'a yi taron kasancewa har zuwa wannan lokaci ba'a fara hada rumfarba, amma ana gudanar da aiki ba kama hannun yaro.
An ga jami'an tsaro na yansandan ganowa da kwance bamabamai suna gudanar da aiki a wannan fili.
Gwaamna Bagudu yana daya daga cikin Gwamnonin Arewa da ke dadi da shugaba Buhari, wanda bayanai suka nuna ya samo asali bisa dagewa da jihar Kebbi ta yi wajen noman shinkafa da ya jawo ma Najeriya daraja a fuskan kasashen Duniya, kuma haka ya faranta ran shugaba Buhari.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi