Katin Zabe PVC Shine Makaminku Ranar Zabe - Yekuwan KDF A Masarautar Zuru

Dandalin ci gaban jihar Kebbi watau Kebbi Development Forum KDF wacce ke yekuwa kan wayar da kan jama'ar jihar Kebbi domin zaburar da yan kasa saboda su zaba ma kansu matanen kwarai a zabuka da ke tafe domin fitar da shugabanni a matakai daban daban ta hanyar jefa kuri'a. KDF tare da hadin guiwa da kungiyar cigaban matasa Barewa Youth Initiative da sauran kungiyoyi ta gudanar da taron yekuwa a Masarautar Zuru ranar Alhamis.

Yayin gabatar da jawabinsa shugaban kungiyar KDF na jihar Kebbi Profesa S.D Mahuta ya yi jawabi kan manufofin kungiyar da suka shafi wayar da kan jama'ar jihar Kebbi. "KDF wata kungiya ce mai zaman kanta ba ta gwamnati bace, KDF ta kunshi dattiai da kwararru yan asalin wannan jiha masu kishin kai da kuma kishin jihar Kebbi da Najeriya gabadaya" Profesa ya ce "wadanda basu karbi katin zabe PVC ba su kokarta su je su karba".

Ya kuma ce ranar jefa kuri'a fito gabadaya a je a kada kuri'a. Profesa S.D Mahuta ya ce "Gwargwadon yawan jama'a gwargwadon muhimmancin da dan suyasa zai ba al'umma. Lokacin kada kuri'a a sa kishin kasa domin kuri'a 'yancinka ce. Mu canza daga kuri'ar meye zan samu daga dan takara. Kuri'arka tamkar Remote Control ne na Talabijin, da ita za ka yi zabe kuma da ita za ka iya kiranye idan dan siyasa bai bayar da ingantaccen wakilci ba, mu yawaita tuba ga Allah.

Shugaban kungiyar cigaban kasar Masarautar Zuru kuma tsohon Ambassada Yakubu Kwari, ya bukaci jama'a su kasance masu amfani da abin da aka tattauna a wannan taro ta yekuwa da kasancewa a shirye gabanin zaben 2019. Ya kara da cewa mallakar katin zabe ke da mahimmanci. "Ina son in shaida maku cewa ba za ka iya zaben mutum ba idan baka da katin zabe PVC . Ku tabbatar da cewa kun rike PVC naku domin shi ne makaminku. Kada ku yarda wani ya rudeku domin ku yi tashi hankali.Idan baku karbi PVC naku ba, ku hanzarta ku je INEC ku karbi PVC domin shi ne makaminku a ranar zabe".

Babban jami'in dansanda mai kula da shiyar Masarautar Zuru D.C.P Hayatu Usman ya yi jawabi kan yadda 'yansanda suka shirya tsaf domin tunkarar zaben 2019 a Masarautar Zuru. Ya kuma bukaci jama'a su bayar da hadin kai ga jami'an tsaro. Ya kara da cewa " duk yadda jami'in tsaro ya so ya gudanar da aiki, idan jama'a basu bashi hadin kai ba, ba zai yi nassara ba a kan aikinsa".

Daga karshe, Mai Mairtaba Sarkin Zuru Maj.Gen Muhammadu Sani Sami2, wanda Sarkin Rikoto Alh Shehu Muhammad Bandi, ya yi karin haske ne bisa ga muhimmancin karban katin zabe PVC, ya kuma bukaci jama'a su gaggauta karban katin zabe kafin ranar zabe. Hakazalika ya bukaci jama'a su zabi shugabanni na gari, kuma su je su kada kuri'a ranar zabe.

Daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da shugaban kungiyar ci gaban Masarautar Zumu Ambasada Dr Yakubu Kwari, shugaban Dandalin ci gaban jihar Kebbi KDF, Kwamandan rundunar 'yansanda shiyar Masarautar Zuru, Sakataren KDF, wakilin Maii Martaba Sarkin Zuru wanda shi ne Sarkin Rikoto, babban jami'i a kungiyar Barewa Youth Initiative da sauran masu jawabi.

Taron ya sami halarcin Wakilin Mai Martaba Sarkin Zuru, watau Sarkin Rikoto Alhaji Shehu Muhammad Bandi, shugaban ZEDS Ambasada Dr Yakubu Kwari, shugaban dandalin ci gaban jihar Kebbi KDF Profesa S.D Mahuta, Ubannin kasa da Hakimai, Kwamnadan yansanda shiyar Zuru D.C.P Hayatu Usman tare da sauran DPO na rundunar shiyar Zuru, Mukaddashin Kwamandan Bataliyan soji na 223 na Barikin Dakkarawa, Daraktan ilmantar da jama'a kan harkan zabe na INEC Adamu Musa, shugabanni da wakilan sauran kungiyoyi da sauran manyan baki.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN