2019: Karanta Abin Da Zai Faru Idan Kana Da Katin Zabe Amma Baka Kada Kuri'a Ba - KDF Da INEC

isyaku.com 21-01-2019

Kungiyar DKF watau Kebbi Development Forum ta gudanar da taron fadakarwa da kuma yekuwa domin tunatar da jama'a kan muhimmancin mallakar Katin zabe na dindindim Permanent Voters Card PVC a Masarautar Argungu ranar Litinin 21 ga watan Janairu 2019. Tawagar karkashin jagorancin Profesa M.D Sahabi, ta kai ziyarar bangirma ga Mai Martaba Sarkin Kabi a Fadarsa da ke cikin garin Argungu wanda Kundan Kabi Alh. Ibrahim Hassan ya wakilta.


Prof. D.M. Sahabi ya yi takaitaccen jawabi kan makasudin ziyara da kungiyar ta kai a Fadar Sarkin Kabi.

A nashi jawabin maraba ga tawagar KDF zuwa Masarautar Argungu, Kundan Kabi Alh Ibrahim, ya gode ma tawagar tare da fatan Allah ya sa alhairi a cikin lamarin, hakazalika ya yaba wa kungiyar KDF tare da sauran kungiyoyi da suka yi hadaka suke tafiyar da shirin fadakar da al'umma.


Bayan ziyarar bangirma a Fadar Sarkin Kabi, tawagar ta zarce zuwa dakin taro na Masarautar Kabi, inda ta ci gaba da gudanar da taron fadakarwa wanda shugaban kungiyar KDF Pro.D.M Sahabi ya faraa gabatar da jawabinsa na ilmantarwa kan muhimmancin mallakar katin zabe. Prof Sahabi ya ce "Mallakar katin zabe yana da muhimmanci domin idan baka je ka yi zabe ba a ranar zabe, sai wasu su zaba maka wanda bakaso kuma dole ka yi hakuri".

Add caption

Bayanai daga bakin wani babban jami'i daga hukumar zabe mai zaman kanta INEC Alhaji Adamu Musa, ya ce fiye da mutum Miliyan daya da dubu dari takwas da dari biyu da daya ne INEC ta yi ma rajistan katin zabe a jihar Kebbi. Amma akwai fiye da dubu dari biyu da ba'a karba ba har yanzu a fadin jihar ta Kebbi.

Alhaji Musa ya yi karin haske ga mahalarta taron kan

1. Fa'idar gaggautawa domin a karbi katin zabe kafin a rufe karban kati

2.  Kana da hakkin ka kada kuri'a kuma ba atare da wata tsangwama ko barazana daga kowa ba

3. Katin ka na zabe shine 'yancin ka na zaben wanda kake so, kuma da shi ne za ka yi amfani domin a kira wanda ka zaba idan ya kasa aikata abin kirki

4. Tabbatar da sirrinka a lokacin zabe, ta yadda ba wanda zai san jam'iya ko dan takara da ka zaba

5. Kada ka tayar da hankalin jama'a a wajen zabe ko wajen kada kuri'a.

7. Ka bi doka da oda a wajen zabe, ban da tayar da hankalin jama'a, satar akwatin zabe, saye ko sayar da kuri'a da dai sauransu.

ASP Aminu Musa, jami'in 'dansanda ne da ya wakilci hukumar 'yansanda a wajen taron daga ofishin 'yansanda na karamar hukumar Argungu, ya bayyana shirin da 'yansanda sukayi tsaf, domin tabbatar da sun bayar da tsaro kamar yadda aka saba a wannan zabe da ke zuwa. Ya kara da cewa " Aikin tabbatar da tsaro aikinmu ne, kuma DPO ya ce Kwamishinan yansanda ya shida masa cewa za a karo jami'an tsaro zuwa Masarautar Argungu domin su taimaka wajen bayar da tsaro a lokacin zabe".


Uban Kasar Gulma Alhaji Muhammad Bashar Gulma, wanda shi ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin Kabi a wajen taron, ya bukaci a taimaka wa mutane masu matsala da mata masu dauke da juna biyu domin a yi masu layinsu daban, kuma a bari su fara kada kuri'a kafin sauran jama'a su kada nasu kuri'ar. Hakazalika ya bukaci KDF da INEC su kai wannan yekuwa har cin karkara domin jama'a su amfana da kalaman fadakarwa da aka yi bayani a kai a wajen wannan taro.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN