Type Here to Get Search Results !

Main event

Buhari Ya Karrama Sojojin Da Suka Mutu A bikin Tuna Mazan Jiya A Abuja. Hotuna


Legit Hausa

Ana gudanar da wannan biki ne a duk fadin duniya a ranar 11 ga watan Nuwamba don tunawa da ranar da yakin tunawa karshen yakin Duniya na daya, tare da Sojojin da suka mutu, sai dai Najeriya ta canza nata ranar zuwa 15 ga watan Janairu, ranar da yakin basasa yak are, 15 ga watan Janairu na 1970.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Osinbajo sun samu halartar bikin da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, inda aka hangesu suna jingine fulawa a matsayin wata hanyar girmamawa ga mamatan.


Haka zalika, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki, Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, Alkalin Alkalai, Ministan Abuja, da Ministan kudi duk ni sawun shugaba Buhari wajen jingine fulawar.

Sauran sun hada da shugaban hafsoshin rundunonin Sojin Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukuru Buratai, babban hafsan Sojan sama, Sadiqque Abubakar, babban hafsan sojan ruwa da tsohon babban sufetan Yansanda, Ibrahim Idris da kuma ministan tsaro Mansur Dan Ali.


Bugu da kari shugaba Buhari ya saki wasu fararen tantanbaru, wani alama dake nuni da zaman layi, sa’annan yayi gabatar da jawabi ga yan uwan mamatan da suka samu halartar bikin, sa’annan ya bi sauran manyan bakin da suka halarta da gaisuwa. Sai dai wasu daga cikin iyalan mamatan da suka halarci bikin sun koka da yadda gwamnatin Najeriya ke nuna musu halin ko in kula game da mawuyacin halin da suka afka tun bayan mutuwar mazajensu ko iyayensu Sojoji.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies