Type Here to Get Search Results !

Zargi: Dattijo ya ki barin a yi ma dansa aikin ido domin da ciwon ne yake neman na cefane

Sani Musa Saminaka
Ana zargin wani magidanci da kin yarda a yi ma dansa mai suna Isa aiki a idonsa na hagu sakamakon tabuwa da idon ya yi da matsanancin rashin lafiya a garin Yauri na jihar Kebbi.

Wata majiya ta shaida mana cewa, wasu jama'a sun yi kokari domin ganin sun hada kudi su taimaka ma wanna yaro domin a kai shi Asibiti a Kaduna, inda ake kyautata zaton cewa Likita zai duba yaron.

Bayanai sun tabbatar da cewa wani dan uwan sa ya bayar da kudi masu dama domin taimakon yaron, hadi da wasu kudade da wasu matasa suka hada domin taimakawa, daga bisani aka kai yaron wani Asibiti a Kaduna. Majiyar mu ta shaida mana cewa a daidai lokacin da Likita ya nemi amincewar Mahaifin yaron mai suna Malam Sulaiman domin ya sa hannu a takardun Asibiti kafin a yi ma yaronsa Isah aiki, sai fa mahaifin Isa watau Mal. Sulaiman ya ce alam baram ba zai sa hannu ba.

Bisa wannan dalili ne fa lamari ya cije, domin dai Likita ba zai yi ma Isah aiki a idonsa ba sai mahaifinsa Mal. Sulaiman ya sa hannu a takardun Asibiti, wanda zai nuna cewa da amincewarsa ne aka yi ma dansa Isah aiki.

Wannan lamari ya sa ala tilas zancen ya kai Fadar Mai Martaba Sarkin Yauri Dr.Muhammad Zayyanu Abdullahi, bayan duk kokari da aka yi domin samun amincewar Malam Sulaiman ya bari a yi ma dansa aiki ya ci tura, amma wakilinmu Sani Musa Saminaka ya shaida mana cewa kalaman da wannan dattijo ya bayar a zaman hujja da ya sa bai bari a yi ma yaron aiki ba ya ba kowa mamaki.

"Wannan dattijon ya ce lallai shi yanada wani Malami da yake yi masa aiki ko yaushe , shi ya tabbatar mashi da cewa idan ya bari aka yi ma wannan yaron aiki, to fa akwai matsala , saboda haka gaskiya shi idan har ba an fi karfinsa bane, ba zai yarda a yi ma wannan yaron aiki ba !.

Sakamakon wannan lamari da kalaman da wannan dattijo ya bayar a zaman hujja da ya sa ya ki bari a yi ma dansa Isa aiki ba a idonsa da ke ciwo, ya haifar da zargi mai karfi daga jama'a, wadanda ke rade-radin cewa ba mamaki mahaifin yaron yana amfani ne da rashin lafiyar wannan yaro domin ya dinga neman taimako daga jama'a.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN