Laifi ne yin arziki a mulkin Buhari - Sheikh Gumi


Legit Hausa

Jaridar Thisday tayi wata hira mai tsayi da malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, a kan harkokin da suka shafi kasa da kuma batutuwa masu alaka da zaben shekarar 2019. Da yake amsa tambaya a kan irin shawarar da zai bawa 'yan siyasar Najeriya, Shehun Malamin ya shawarci 'yan takara su saka bukatar kasa a gaba a cikin manufofinsu na yakin zabe.

Da aka tambayi Sheikh Gumi ko mai zai ce a kan shawarar da shugaba Buhari ya bawa malaman addini a kan su nesanta kansu daga harkokin siyasa domin kare mutuncinsu, sai ya kada baki ya ce, "a'a, abinda yake son fadi a fakaice shine malaman addinin Islama da Kirista su daina sukar sa.

Idan ba zamu yaudari kan mu ba, mun san cewar malaman addini mutane ne kamar kowa kuma suna da bukatu kamar yadda ragowar jama'a keda su; suna son ganin an samu shugabanni nagari da zasu taimaki al'umma bakidaya. Na san tabbas akwai malaman dake fakewa da addini domin biyan bukatar kansu, amma akwai wadanda kishin kasa ne a gabansu.

Gumi ya musanta cewar yana sukar gwamnatin shugaba Buhari da yawa, tare da bayyana cewar ya dade yana sukar gwamnatoci a baya kuma ba zai daina ba sai an samu gyara a yadda ake tafiyar da gwamnati a kasar nan.Sai dai, ya ce gwamnatin Buhari na yaudarar jama'a ne kawai da batun yaki da cin hanci bayan a zahiri sun mayar da yin arziki a lokacin mulkinsu laifi.

Kazalika ya soki gwamnati a kan cigaba da tsare shugaban mabiya mazahabar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da kuma artabu da nagoya bayansa dake zanga-zangar neman sakinsa, yana mai bayyan cewar mabiya Shi'a 'yan kasa ne kamar kowa dake da hakkin yin addininsu kamar kowa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN