Tattakin Maulidi a Birnin kebbi, a kwaikwayi halayen Annabi, ayi addu'a a zauna lafiya- Khadi Saddiq

Isyaku Garba -Birnin kebbi - 15-12-2018

 An gudanar da tattaki da kuma Maulidi a garin Birnin kebbi, wanda ya dau hankalin gaba dayan garin Birnin kebbi da ya dau haske da murna daga dandazon jama'a maza da mata da suka yi jerin gwano a manyan titunan garin Birnin kebbi da safiyar Asabar 15 ga watan Disamba 2018, inda jama'a ke tafe suna Salati ga Manzon Allah, wasu kuma na rewa wakokin yabo da begen tsabar kauna da soyayya ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW.

Mauludin na bana 2018 a jihar Kebbi, an tafiyar da shi ne Khalifa baya gari domin yana kasar Saudiya wajen Umrah, sakamakon haka Mai shari'a Khadi Alhaji Saddiq Usman Muhktar ya jagoranci Mauludin na bana a jihar Kebbi wanda aka gudaanar bisa ingantaccen tsari da wadata yanayi tafiyarwa kuma cikin nassara.

Gaba dayan Zawiyoyi da Madrasa na Alkur'ani karkashin mabiya Darika suka halarci wannan tattaki na Mauludi. Hakazalika, an gan wasu masu sana'oin hannu su ma sun shiga wannan tattaki a matsayinsu na mabiya Darika.Wani abin burgewa shine yadda dubu dubatan jama'a maza da mata suka nuna rashin gajiya a wannan tattaki saboda kaunar Annabi, domin dai tun daga randabawal na zuwa gidan Gwamna watau GRA, har zuwa randabawal na Asibitin Sir Yahaya, ya dauka har titin Fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu, zuwa randabawal na zuwa babbar Kasuwa wajen gaban Asibitin Godiya jama'a na kan wannan jerin gwano.

Mai shari'a Khadi Alhaji Saddiq Usman Muhktar ya yi nasiha ga dandazon jama'a da suka halarci wannan Mauludi da tattaki cewa "Annabi ya fi kowa kuma ya fi komi, saboda haka taro domin shi ya fi kowane taro.Wannan kara nuna soyayya ne ga Annabi, kuma a kwaikwayi halayen Annabi. Annabi mutum ne mai gaskiya, mutum ne mai hakuri, mutum ne mai rikon amana, mutum ne mai tausayi.

Khadi Saddiq ya kara da cewa "A yawaita salati ga Annabi, kowa ya tsaya sosai ya yi wa kansa addu'a, da yan'uwansa, da garinsu, da kasarsu. A yi wa kasa addu'a, domin bamu da wata kasa face wannan kasar tamu, domin idan al'amari ya lalace a kasarnan, mu ne abin zai shafa. Saboda haka kowa ya yawaita addu'a domin neman zaman lafiya a wannan kasar".

"A ci gaba da yi wa uwaye da'a, da shugabanni, su kuma mata su girmama mazajensu. Ta wannan hanya ma za'a samu zaman lafiya".

"Siayasa da ke tafe kuwa, kada ayi abin da zai kawo tashin hankali, idan mutum ya yi abin tashin hankali, kuma ba za ta kyale shi ba don haka a zauna lafiya.

Khalilifa ya yi tafiya yana wajen Umrah, shi ne ya sa na tsaya madadinsa Mai shari'a Khadi Alhaji Saddiq Usman Muhktar, daga karshe ya shaida ma Mujallar isyaku.com cewa "Makasudin wannan tattaki da Maulidi na bana shine a kwaikwayi halayen manzon Allah, a zauna lafiya, a yi addu'a, a kuma yi wa kasa addu'a shine makasudin wannan Mauludi na 2018 a cikin garin Birnin kebbi a jihar Kebbi. Ba wai a yi taro a watse ba, ba tare da tunawa da Annabi da halayensa ba".

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN