Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC a jihar Anambra Sunday Ajayi ya mutu a wani mumunar hadarin mota.
Mr. Ajayi ya mutu ne da safiyar yau a garin Agbor na jihar Delta yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga jihar Kwara inda ya halarci wani daurin aure. Saidai Mujallar isyaku.com ya jiyo cewa derebansa Marshal Raji ya tsira kuma yana Asibiti yana jinya.
Hafsoshi da ma'aikatan FRSC na jihar Anambra har da jama'ar gari masu ababen hawa suna matukar kaunar Mr.Ajayi, sakamakon saukin kai da kirkire-kirkire da tsare-tsaren kula da ka'idodi da dokokin hanya a jihar Anambra.
Wata majiya ta shaida mana cewa marigayin yana tare da jama'arsa a gidan Radio na Anambra Broadcasting Service (ABS) ranar Juma'a 14/12/2018.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi