'Yan takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC ne INEC ta
bayyana cewar sun yi nasara a zaben maye gurbi da aka yi a jihohin Bauchi,
Katsina, da Kwara. A jihar Katsina, Abubakar Kusada na jam'iyyar APC ne ya
lashe zaben maye na mazabar Kankia/Kusada/Ingawa. Kusada ya samu kuri'u 48,518,
fiye da na dan takarar da ke biye ma sa, Abdulssamad Yusuf na jam'iyyar PDP.
Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Rasheed Adebayo,
baturen hukumar zabe, ya sanar da cewar Kusada ne ya lashe zaben bayan samun
kuri'u ma fi rinjaye. Yusuf Nuhu, dan takarar jam'iyyar APC, ne ya lashe zaben
maye gurbin kujerar dan majalisar wakilai na mazabar Toro a jihar Bauchi. Dan
takarar na APC, Yusuf Nuhu, ya samu kuri'u 22,317 yayin da Shehu Buba na
jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 18,235. Nuhu ya samu nasara a mazabu 11, yayin da
Buba ya lashe mazabu 3 kacal.
Legit hausa
Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Ahmad Tijjani
Fagam, ya ce dan takarar jam'iyyar APC ne ya lashe zaben saboda ya samu kuri'u
ma fi rinjaye. A daren jiya, Asabar, ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya
bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaben maye gurbi na
kujerar majalisar wakilai ta mazabar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero.
Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abimbola Adesoji,
baturen zabe na hukumar INEC, ya bayyana cewar APC ta samu kuri'u 21,236 yayin
da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 18,095. Ya kara da cewar Labour party ta samu
kuri'u 150, jam'iyyar PPN ta samu kuri'u 76, sai kuma jam'iyyar UPN da ta samu
kuri'u 42. Farfesa Adesoji ya ce an kada jimillar kuri'u 40,930 a zaben, adadin
kuri'u 1,331 ne su ka lalace.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI