Legit hausa
Wata kotu dake zaman ta a garin Abuja mallakar gwamnatin
tarayya ta kori karar da wata kungiyar 'yan madigo ta shigar a gaban ta suna
kalubalantar hana su satifiket da hukumar yiwa kungiyoyi da kamfuna rijista
watau Corporate Affairs Commission (CAC) a turance ta ki yi masu.
A zauren kotun, Mai shari'a Nnamdi Dimgba, ya bayyana cewa
matakin da hukumar ta CAC ta dauka na kin yi mau rijista yayi daidai da dokokin
da suka kafa hukumar musamman ma na sashe na 30 (1) (c) a kundin dokar da ta
kafa ta na 2004.
Legit.ng Hausa ta samu cewa tun farko dai wata babbar shakiyyiya ce mai suna Pamela Adie ta shigar da karar biyo bayan kin yiwa kungiyar ta ta 'yan madigo da kare hakkin su da ta sawa suna “Le3bian Equality and Empowerment Initiatives” da turanci rijista da hukumar ta CAC tayi.
Legit.ng Hausa ta samu cewa tun farko dai wata babbar shakiyyiya ce mai suna Pamela Adie ta shigar da karar biyo bayan kin yiwa kungiyar ta ta 'yan madigo da kare hakkin su da ta sawa suna “Le3bian Equality and Empowerment Initiatives” da turanci rijista da hukumar ta CAC tayi.
A wani labarin kuma, Hankula sun tashi a garin Awka, babban
birnin jihar Anambra yayin da aka kama wani matashi mai shekaru 19 kacal a
duniya mau suna Sunday Owo da ya ziyarci wata asibitin gargajiya da sassan
jikin mutane da kuma kwalba cike da jini kulle a cikin buhu. Kamar yadda muka
samu, matashin ya fito ne daga karamar hukumar Ohaukwu ne ta jihar Ebonyi dake
makwaftaka da jihar ta Anambra kuma kamar yadda yace, ya zo ne neman maganin
yin kudi ko ta halin ka-ka.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI