Jihar Niger ta amshe lamba daya wajen noman shinkafa

isyaku.com 4-11-2018

Babban jami'i da ya jagoranci jihar Niger wajen nuna kayakin amfanin gona da aka kammala kwanakinnan ya bayyana dalili da ya sa jihar Niger ta zama na daya wajen noman shinkafa sakamakon bayani da hukumar National Agricultural Extension and Research Liaison Services (NAERLS) na Jami'ar Ahmadu Bello  (ABU), Zaria ta fitar ya ce hakan ya samu ne sakamakon tallafi da manoma suka samu bisa adalci. Dr. Aliyu Usman Kultigi ya bayyana haka wanda shi ne shugaban shirin Fadama III na jihar Niger.

Dr. Kutugi ya ce a karkashin shirin Fadama III, manoma 11.000 ne masu hectare 1 suka sami tallafin da ya dace sakamakon haka suka noma hectare 11.000.

Hakazalika ya ce an samar da filayen aikin noman rani guda 6 wanda hakan ya tabbatar da samar da wadataccen shinkafa da dai sauran ingantattun tsare-tsare da ke tafiya bisa tsari da ka'ida.

Jihar Kebbi dai ta sha yin kuri da harkar noman shinkafa kuma tuni mahukuntar jihar Kebbi suka mayar da hankali wajen watsa labarai da suka shafi harkar noman shinkafa kasancewa shugaba Buhari ya hankalta da harkar noman shinkafa a jihar Kebbi. Amma a lokaci daya kuma, wasu al'ummar jihar Kebbi na kallon shirin a matsayin harkar siyasa.


DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN