Fiye da mutum miliyan 2 ne suka ziyarci Mujallar ISYAKU.COM, ga sako

Mujallar ISYAKU.COM tana yi wa masoyanmu masu ziyartar shafin mu godiya bisa yadda suke biye da mu a cikin labaran mu wanda hakan ya sa muka ci ma adadin fiye da mutum miliyan 2 da dubu arba'in da kari kawo yanzu mutum 2047426 ne suka ziyarci shafin kuma adadin maziyarta na karuwa a kullum..

Shakka babu mun fi bayar da himma ga labaran al'ajabi wanda shi ne jama'a suka fi kauna bisa sakamakon bincike da muka gudanar a kan ko wadanne irin labarai ne aka fi karantawa idan mun wallafa.

Muna farin cikin shaida maku cewa sashen jakar magori ne aka fi karantawa, sai kuma labaran siyasa. Dalili da ya sa bamu faye bayar da labaran zube ba shine ISYAKU.COM Mujalla ce, wacce za ta iya bayar da labari daga daya a rana zuwa abin da ya sauwaka. Amma jaridau kan dauko labarai fiye da 20 ko 40 a rana, amma mun lura cewa sakamakon moriyar yanar gizo na zamani, kusan labari daya Jaridu 50 za su iya maimaita shi.

Sakamakon haka ya sa muka dukufa wajen nishadantar da al'umma wajen kawo masu labari da ba kowane Jarida ce za ka ga labarin a cikinta ba, kuma mukan saka hotunan abin da muka bayar da labari a kansa domin mai karatu ya hankalta kuma ya zama izna ga wasu.

Mujallar ISYAKU.COM tana da hurumin yin bincike kan lamurar da ke da sarkakiya a cikin al'umma, musamman takan dauko labarai da manyan Jaridu ke kaucewa da gangan saboda su sai an bayar da ihsani mai kauri, amma a ISYAKU.COM mukan kwatanta adalci, kuma muna dauko labarn jinkai kuma domin neman lada.

Muna amfani da wannan damar domin mu yi kira ga matasa yan Arewa cewa kada su jira sai gwamnatocin jihohin Arewa sun basu aiki a gidajen radiyo ko talabijin na jihohinsu, amma ku yi amfani da karatunku na jarida  Mass Com domin sama wa kanku aiki ta hanyar bude shafukan Mujalla a yanar gizo . Manyan mawallafa a yanar gizo a Najeriya kamar Lindaikejisblog, Lailasnews, Ogbongeblog da sauransu ai sunayensu ne suka saka. Ba wai sai ka ce BBC ko VOA ne kafafen labarai ba kawai. Legit hausa,Mujallarmu,Alummata da sauransu ai ba kafofin labarai na gwamnati bane kuma suna bayar da ingantattun labarai.

Mun gode, daga Mawallafin isyaku.com

Isyaku Garba


DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN