Mama Taraba ta amshe kayaki da ta ba jam'iyyar APC gudunmuwa a Taraba

Jamiyyar APC a jihar Taraba ta zargi tsohuwar Ministan Mata Sanata Aisha Jimmai Alhassan da aikata abin kunya bayan ta bukaci a cire kuma a bata duk kayakin da ta bayar zaman gudunmuwa ga Sakatariyar jam'iyyar a Jalingo na jihar Taraba.

Kakakin jam'iyyar APC na jihar Taraba Mr. Aaron Artimas ya shaida wa yan Jarida cewa, tsohuwar Ministan ta bukaci a ba ta duk wani abu da ta ba jam'iyyar, sakamakon haka kuma, jam'iyyar ta aminta ta cire kayakinta domin a rabu lafiya. Kayakin da ta cire sun hada da Kapet na shifida a kasa, Kwamputoci, na'urar sanyaya daki AC da sauransu.

Aisha Jimmai Alhassan wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta ce ta sayi kayakin ne da kudinta, kuma sakamakon rashin adalci da ta fuskanta a hannun jam'iyyar APC shi ya sa zata karbi kayanta. Mama Taraba ta raba gari da gwamnatin APC bayan ta yi zargin an aikata mata ba daidai ba a wajen zaben fitar da gwani na takarar kujerar Gwamna a jihar Taraba.

Hakazalika, Mama Taraba ta fice daga jam'iyyar APC , ta yi murabus daga mukaminta na Minista, daga karshe ta yar da kwallon Mangoro domin ta huta da kuda ta hanyar ficewa daga jma'iyyar APC ta koma jam'yyar UNDP.


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN