Type Here to Get Search Results !

Yin rawa tsirara a Birnin kebbi, Kotu ta adana maza da 'yan mata 14 a Kurkuku

Wata Kotun Majestare karkashin Mai shari'a Halima Abubakar da ke zamanta a garin Birnin kebbi, ta tasa keyar wasu mutum 14 zuwa Kurkuku domin adanawa kafin zaman Kotu na gaba. Mutanen sun gurfana a gaban Kotun ne bisa zargin yin rawa tsirara, tayar da hankalin jama'a da sauransu.

Mai gabatar da kara Yakubu Goje, ya shaida wa Kotu cewa jami'ai sun kama wadanda ake zargi ne a karkashin wata gada da kayakin kida tare da 'yan mata suna holewa, a gefe daya kuma, wasu na zukar wani abu da ake zargin ababen sa maye ne.

Wadanda aka kama maza tara da mata biyar, mai gabatara da kara ya ce wadannan matasan sun yi ma wasu jami'ai biyu rauni sakamakon yadda suka far masu da adduna kuma suka lalata motar su ta sintiri a daidai lokacin da motar jami'an ta isa wajen da ake holewar.

Bayan ta saurari jawaban mai gabatar da kara, mai shari'a Halima Abubakar ta bayar da umurni a tasa keyar wadanda ake zargi zuwa Kurkuku kafin zaman Kotu na gaba.

Daga Isyaku Garba

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN