Gaya mana me kayi da bashin N13Tr da ka ciwo a shekaru ukku - Atiku ga Buhari

Mai neman shugabancin kasa kasa ta karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana yanda ya kashe Naira tiriliyan 13 da ya ranto a cikin shekaru uku na mulkin shi. Yace Naira tiriliyan 6 kacal PDP ta ranto amma ana ta cece ku ce. A jawabin da tsohon mataimakin shugaban kasar yayi ta bakin kungiyar yakin neman zaben shi a Abuja a ranar laraba, ya zargi APC da rashin aikin yi ta yanda suka bar lamarin shugabancin da sauke hakkokin su, inda suka fi maida hankali da zargi tare da karairayi ga Dan takarar shugabancin kasa na PDP. "Domin ba wa yan Najeriya ansa, muna so kungiyar yakin neman zaben Buhari da su dauki kalubalen nan ta hanyar ansa wadannan tambayoyi." "Ku sanar damu aiki daya da Gwamnatin Buhari ta kirkiro, ta fara kuma ta gama a shekaru uku da suka wuce." "Ku sanar damu matashi daya da yake a Gwamnatin shugaban." "Ku fadi alkawari daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika." "ku fada mana suna Dan kudu daya da ke shugabancin cibiyar sirri ta kasa." "Ku fadi Dan ta'adda daya da aka kama, aka kai shi kotu kuma aka daure shi a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari," ya rufe. Atiku ne dai ake sa rai zai baiwa APC babban aikin kayar dashi a badi a zaben shugaban kasa. Read more: https://hausa.naija.ng/1197605-gaya-mana-kayi-da-bashin-n13tr-da-ka-ciwo-a-shekaru-ukku-atiku-ga-buhari.html#1197605
Mai neman shugabancin kasa kasa ta karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana yanda ya kashe Naira tiriliyan 13 da ya ranto a cikin shekaru uku na mulkin shi.

Yace Naira tiriliyan 6 kacal PDP ta ranto amma ana ta cece ku ce. A jawabin da tsohon mataimakin shugaban kasar yayi ta bakin kungiyar yakin neman zaben shi a Abuja a ranar laraba, ya zargi APC da rashin aikin yi ta yanda suka bar lamarin shugabancin da sauke hakkokin su, inda suka fi maida hankali da zargi tare da karairayi ga Dan takarar shugabancin kasa na PDP.

"Domin ba wa yan Najeriya ansa, muna so kungiyar yakin neman zaben Buhari da su dauki kalubalen nan ta hanyar ansa wadannan tambayoyi." "Ku sanar damu aiki daya da Gwamnatin Buhari ta kirkiro, ta fara kuma ta gama a shekaru uku da suka wuce.

" "Ku sanar damu matashi daya da yake a Gwamnatin shugaban." "Ku fadi alkawari daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika." "ku fada mana suna Dan kudu daya da ke shugabancin cibiyar sirri ta kasa."

"Ku fadi Dan ta'adda daya da aka kama, aka kai shi kotu kuma aka daure shi a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari," ya rufe. Atiku ne dai ake sa rai zai baiwa APC babban aikin kayar dashi a badi a zaben shugaban kasa.


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN