Type Here to Get Search Results !

Zamu tsige Saraki a matsayn shugaba, sannan mu fatattake shi daga majalisar dattawa – Omo-Agege


Sanata mai wakiltan yankin Delta ta tsakiya, Ovie Omo-Agege, ya sha alwashin cewa shi da sauran sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), zasu tabbatar da cewar an dakatar da shugaban majalisar dattawa kuma sanata mai wakiltan Kwara ta tsakiya, Dr BuklaSaraki daa kujerarsa sannan su fatattake shi daga majalisar dattawa.

Sanata Omo-Agege ya kuma zargi Saraki da shirya makirci don tsige Shugaba Muhammadu Buhari inda ya kara da cewa indai har shi da sauran sanatocin APC na majalisar dattawa, baza’a yi nasara ba a duk wani yunkuri na tsigeBuhari. Ya bayyana hakan a Sapele, jihar Delta lokacin day a ai ziyarar zanawa da shugabanni, dattawa da kuma shugabannin kananan hukumomi na APC a yankin Delta na tsakiya a kokarin shin a sake neman goyon bayansu a zabe mai zuwa.

A wai lamari na daban, mun ji cewa yan takara a karkashin jam’iyyar APC na ci gaba da nuna dari-dari da shuwagabannin jam’iyyar, biyo bayan tsadar kudin tikitin tsayawa takara da jam’iyyar ta sanar. Rahotannin da NAIJ.com ta tattara a Abuja, a ranar asabar, na nuni da cewa yan takara a jam’iyyar, da suka nuna sha’awar tsayawa takara a matakin gwamna, majalisun dokoki na kasa da ma shugaban kasa, na bayyana damuwarsu bisa tsadar da tikitin yayi. Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage kudaden da aka sanya.

A baya bayan nan ne dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC, ya fitar da kudin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa akan Naira Miliyan 55, wanda ya haura Naira Miliyan 12 da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN