Wasu yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples
Democratic Party, PDP, wadanda suka kasance a cikin jam’iyyar tun shekarar 2014
sun yi gargadi ga shugabannin jam’iyyar kan baiwa wadanda suka dawo jam’iyyar
bayan sun fita a 2014 fifiko akansu.
Yayinda suke wannan gargadi, sun bayyana cewa wadanda suka
ki sauya sheka a 2014 ne suka rike jam’iyyar lokacin da wasu suka fice kuma
suka taimaka aka kayar da jam’iyyar a shekaran 2015, saboda haka, su ya kamata
fifita ba baki ba. Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki; tsohon
mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; gwamna Aminu Waziri Tambuwal, da
tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na daga cikin wadanda suka
dawo jam’iyyar daga APC.
Komawarsu APC ya taimaka matuka wajen nasarar da shugaba
Muhammadu Buhari ya samu a shekaran 2015. Yayinda ake shirye-shiryen zaben
fitar da gwanin jam’iyyar PDP, mutane biyar daga cikin yan takaran shugaban
kasan da basu taba sauya sheka ba sun hada baki domin hada kawunansu wajen
tabbatar da cewa daya daga cikinsu ne zai samu nasara. Ganawar game da wata
majiya mai karfi, za’ayi ne domin jawo hankalin ‘deleget’ da kwamitin
gudanarwan jam’iyyar kan yadda za’a zabi mutum daya wanda bai bata sauya sheka
ba daga cikin yan takaran jam’iyyar 13.
Tsohon shugaban jam’iyyar, Ahmed Makarfi; tsohon minister,
Tanimu Turaki; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon gwanan jihar
Plateau, Jonah Jang; gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dakwambo; za su gana a Abuja
wannan mako
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng