Uwar jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta yi yanke shawarar yin
fatali da tsarin fidda gwani na zaben kato bayan kato, inda ta bayyana burin
yin amfani da zaben fidda da gwani ta hanyar yin amfani da wakilan
jam’iyya.
NAIJ.com ta ruwaito shugaban APC na jihar Kaduna, Emmanuel Jekada ne
ya sanar da haka bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ranar
Alhamis, 6 ga watan Satumba a garin Kaduna.
Shugaba Jekada ya bayyana cewa da dama daga cikin
shuwagabannin jam’iyyar a Kaduna sun goyi bayan yin amfani da tsarin amfani da
wakilan jam’iyya wajen gudanar da zaben fidda gwani a dukkanin mukamai banda na
shugaban kasa.
“Duba da kalubalen
tsaro, kayan aiki da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kaduna,
yawancin yayan jam’iyyarmu sun goyi bayan yin amfani da wakilai wajen zabo yan
takarar da zasu wakilci jam’iyyar APC a mukamai daban daban a zaben fidda
gwani.
“Wannan shine gaskiyar abinda yawancin yayan jam’iyyarmu suka bukata,
basu yarda da zaben kato bayan kato ba, wannan shine sakamakon zaman da muka yi
a yau, don haka nan bada jimawa ba zamu mika rahotonmu ga uwar jam’iyya dake
Abuja.” Inji shi.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai mataimakin
gwamnan jihar Kaduna, mukaddashin gwamnan jihar, Barnabas Bala Bantex, Kaakakin
majalisa, Aminu Abdullahi Shagali, yan majalisun tarayya, yan majalisun dokokin
jiha da sauran masu ruwa da tsaki.
A wani labarin kuma dan majalisa mai wakiltar al'ummar
Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya caccaki manufar jam'iyyar APC ta jihar
Kaduna na yin amfani da zaben wakilan jam'iyya.
Shehu Sani ya bayyana haka ne a
yayin daya jagoranci wata kungiya ta yan takarkaru a inuwar jam'iyyar APC zuwa
babban ofishin uwar jam'iyyar APC dake Abuja, inda ya nuna dacewar yin amfani
da tsarin kato bayan kato wajen fidda dan takara.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng