Harin yan daba kan tawagar dan takarar Sanata a PDP, mutum 1 ya mutu - Hotuna

Wasu yan daban siyasa sun kai wa ayarin motocin wani dan takaran Sanata, Patrick C. Ndubueze daga karamar hukumar Umualumoke Okigwe da ke jihar Imo hari yayin da yake tafiya kan hanyarsa ta yin kampen a yankin Ehime Mbano. Lamari da ya yi sanadin mutuwar mutum daya nan take.

Majiyarmu ta labarta cewa akwai alamar cewa wasu ne suka yi hayan matasan domin su aiwatar da wannan hari, kuma an matukan lalata wasu motocin da ke cikin tawagar har da mota kirar SUV da dan takaran Sanatan ke ciki.

Hon. Patrick Ndubueze ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, daga bisani ya sanar da 'yansanda domin gudanar da bincike. Dan takaran na bukatar tsayawa ne a jam'iyar PDP.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN