Kebbi: Kansiloli sun fara shirin tsige shugaban karamar hukumar Shanga

Sani Musa Saminaka | 22-9-22018 |

Kansiloli na karamar hukumar mulki na Shanga suna neman tsige Ciyaman nasu Hon.Aminu Arzika tungannoma.

Alokacinda wannan rigimar ke motsawa nayi kokari na binciki Shugaban Kansilolin(Speaker) wato Hon.Shamsuddin Isyaku , ko menene dalilin faruwar hakan ?
Hon.Shamsuddini ya zayyana mini laifuka goma-sha-daya (11) wa'yanda suke zarginsa (shi Ciyaman) dasu , ya kuma karamin dacewa abubuwan suna daure musu kai matuka wanda ko yaushe sukayi masa magana sai ya nuna musu cewa baida lokacinsu.

Sun kuma nemi yayi hakuri yazo su zauna dashi domin afahimci inda aka sa gaba , amma ya ki, daga karshema ce musu yayi su dauki duk irin matakinda suke iya dauka ko kuma suyi kararsa. 

Wannan ne dalilinda yasa suka ga babu wani mataki da zasu fara dauka a kanshi kamar wannan , saboda sanin cewa shima yanada shuwagabanni , inhar su basuda wani girma gareshi.

Na kara tambayarsa  cewa kana ganin wannan matakinda kuka dauka yana tasiri kuwa saboda ganin cewa wannan matsalar ta Ciyamomi tayi kusa ta zama ruwan-dare yanzu a wannan Jahar tamu ta Kebbi ?

Yace tabbas suna kyautawa zaton zatayi tasiri, domin za'a kirasu azauna dasu domin warware matsalar.

GADAI LAIFUKANDA AKE ZARGINSA DASU

01 Yana gudanarda harkokin mulki shikadai ba tareda 'yan Majalisarsa ba ko neman shawararsu,
02 Baya zuwa wurin aikinsa (office) domin sauraren matsalolin al'umma saidai idan bukatarsa ta taso,
03 Gwamnatin Jaha ta bayarda Buhuhunan Shinkafa a raba wa Kansiloli da sauran al'umma amma ya raba kadan ya kwashe kaso mai tsoka, mun nemi bayani babu,
04 Gwamnatin Jaha ta bada naira miliyan daya a raba wa Malamai, amma ya bada naira dubu dari biyu da hamsin kawai ya haye sauran,
05 Gwamnatin Jaha ta ware makudan kudade domin yin rijistan zabe, amma ya haye kaso mafi yawa cikin kudin , wasu lokuta ma da kudinmu muke tallafawa masu aikin,
06 Gwamnatin Jiha ta kara ware makudan kudade domin sayen Ragunan Layya ga shuwagabannin siyasa da makamamtansu, amma ya haye kaso mai tsoka kuma babu bayani,
07 Gwamnatin Jiha ta ware miliyan gomashahudu ga wa'yanda ruwa suka yiwa barna a wasu garuruwa cikin karamar hukumar  , amma ya raba kudin yadda yaga dama ba bisa ka'idaba,
08 Gwamnatin Jiha ta ware naira miliyan hamsin domin yin wasu aikace-aikace  a mazabun gundumomi (wards) amma kadan ya bayar kamar yadda za ka gani da idonka ,
09 Daga watan Satumba 2017 zuwa Yuli 2018, baya basu kudin alawus kamar yadda ya dace,
10 Hakazalika bai da kyakkyawar hulda da Kansilolinsa, da ma sauran jama'a baki daya, musamman ma'aikatansa.
11 Kudin overhead cost basu san abinda yakeyi dasuba , kuma babu bayani.
Da wannan muke ganin ya dace garemu mukai kukan mu ga uwayemmu domin samun mafita.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN