'Dugunzumar neman tazarce ta wasu gwamnoni 5 na jam'iyyar
adawa ta PDP ta sanya sun fara shirye-shirye na ƙulla yarjejeniya da shugaban
kasa Muhammadu Buhari, dangane da babban zabe na 2019 kamar yadda shafin
jaridar The Nation ya ruwaito.
Gwamnonin na neman ƙulla yarjejeniya da shugaban kasa ta
goyon bayan tazarcensa ta sake neman kujerar shugaban kasa inda yayin ramawa
Kura aniyarta zai goyi bayan su na komawa kujerunsu a yayin zaben. Sai dai
kamar yadda shafin jaridar ta The Nation ya ruwaito, babu yiwuwar wallafa
sunayen gwamnonin sakamakon wasu dalilai da ta bayyana a matsayin dabaru na
siyasa.
Gwamnonin sun aika gwamnoni biyu na jam'iyyar APC a matsayin
wakilai zuwa ga shugaban Buhari domin shigar da wannan muhimmiyar buƙata, inda
a ranar da ta gabata sakon daya daga cikin su ya isa ga shugaban kasa har
Birnin Sin inda yake halartar taron hadin kan kasar da kuma kasashen Afirka.
NAIJ.com ta fahimci cewa, gwamnonin na neman ƙulla wannan yarjejeniya a
sakamakon fargaba ta rashin samun tazarcen kujerunsu dangane da yadda shugaba
Buhari da jam'iyyar sa ta APC ta fantsama lunguna da sako na kasar nan kamar
yadda wata majiya ta fadar shugaban kasa ta bayyana.
Gwamnonin biyar sun hadar da biyu daga yankin Kudancin Kudu
yayin da sauran biyun suka fito daga yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Kazalika a ranar da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim
Shekarau, ya yi watsi da jam'iyyar PDP inda ake ci gaba da kirdadon sauyin
shekar sa zuwa jam'iyyar mai ci ta APC a yayin da yake ci gaba da tuntube-tuntube
da neman shawarwarin magoya bayansa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng