Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar
zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban
kasa na 2019. Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani
na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.
Jam’iyyar a tsarin gudanarwan tat ace za’a samar dad an takarar shugaban kasa
ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct”kenan a turance.
Ta kuma sanya zaben fidda gwani na gwamnoni zai gudana a
ranakun Litinin, 24 ga watan Satumba da 25 ga watan Satumba. APC a wata sanarwa
daga sakataren tsare-tsarenta, Emma Ibediro, APC ta kuma nuna cewa za’a fara
siyar da fam din tsayawa takara a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba. Jam’iyyar
ta kuma bayyana cewa duk dan takaran kujerar shugaban kasa zai mallaki fam akan
naira miliyan 45 inda aka rage naira miliyan 10 kan yadda yake a baya.
APC ta kuma bayyana cewa yan takaran kujerar gwamna zasu
yanki fam akan naira miliyan 22.5. Yayinda yan takaran kujerar sanata zasu yank
fam naira miliyan 7. Inda yan majalisar wakilai zasu yanki nasu akan naira
miliyan 3.85. Har ila yau yan majalisar dokoki na jiha zasu biya N850,000.
Sannan kuma ana sanya ran yan takara mata da nakasassu zasu biya kaso 50 na
kudin kowani matsayi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng