Yadda wasu matasa suka nagartar da sunan Sanata Adamu Aliero a wajen gajiyayyu

Isyaku Garba | 21-8-2018 |
Kungiyar nan da ke goyon bayan Sanata Adamu Aliero, watau Aliero Support Organisation har ila yau, ta kammala zagayen bayar da taimako da ta yi a kananan hukumomi guda takwas da Sanatan ke wakilta a Mazabar Kebbi ta tsakiya a Zauren masu fararen gemu na Majalisan Dattawa ta Najeriya a birnin Abuja mazaunin Gwamnatin Najeriya.

Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta watau Anas Ibrahim Sanusi Chairman, Shamsu Saidu Aliero Campaign Director , Basiru Muh'd Project Director, da Najashi Muhd V.Chairman sun bayar da taimakon Atamfa ashirin, yadi goma da buhun shinkafa 10kg goma ga jama'ar garin Koko-Besse, wanda wani jigo a kungiyar ta jiha a karamar hukumar Koko-Besse watau Aminu Musa Liman ya karba kuma aka raba wa Marayu da gajiyayyu. Hakazalika, kungiyar ta garzaya babban Asibitin garin Koko inda ta bayar da taimakon kudi ga dukannin marasa lafiya da ke jinya.

Daga nan ne fa kungiyar ta yi burki a Asibitin Aisha Buhari da ke birnin Jega, inda kungiyar ta bayar da taimakon zunzurutun kudi ga duk wanda aka samu kwance yana jinya a wannan Asibiti. Dga bisani, tawagar ta garzaya zuwa cikin birnin na jega ,kuma ta damka wa Najashi taimako wanda shi kuma ya mika wa Marayu da gajiyayyu, kuma fa Najashi bai bar tawagar ta tafi ba sai da ya karanto manyan ayoyin roko daga Alqur'ani, domin neman dacewa ga Adamu Aliero tare da shugaba Muhammadu Buhari. Daga bisani ya yi wa tawagar fatan alhairi.

Kai tsaye sai karamar hukumar Aliero, inda tawagar ta damka kayan taimakon ga Sakataren Izala na karamar hukumar Aliero Malam Faisal Haruna Aliyu, kayakin kamar yadda aka saba su ne atamfa ashiirin, yadi goma da kuma buhun shinkafa 10kg guda goma.

Tirkashi!, aiki ya kammala, abinda ya rage sai neman ijaba da saukan lada daga mai Sammai da Kassai Allah mai komi mai kowa. Haka ta kasance a zagaye na kananan hukumomi takwas da kungiyar Aliero Support Organisation ta yi domin bayar da tallafi gabanin bikin Salar Layya ga al'umma da Sanata Adamu Aliero ke wakilta..

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN