Ruwan sama ya yi sanadin salwantar gidaje 50 a wani gari na jihar Kebbi

Kimanin gidaje 50 ne suka salwanta sakamakon tsananin ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Dakingari da ke karamar hukumar mulki ta Suru a jihar Kebbi. Ruwan ya haifar da ambaliya da ya yi sanadin tabuwar gidajen.

Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa babu asarar rayuwa. Wani babban jami'i a hukumar bayar da agaji na gaggawa a jihar Kebbi Alhaji Rabiu Kamba ya shaida haka.

Kamba ya kara da cewa, hukumar SEMA, tana harhada bayanai na irin asara da aka yi domin ta gabatar wa gwamnatin jihar Kebbi.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN