Assalamu aliakum jama'a, Ni Abu Najakku, dan takara mai neman kujerar Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza, ina taya ku murnar Sallar Layya tare da fatar alheri gareku da iyalanku. Hakazalika, ina yi muku fatar kiyayewar Allah tare da saukar ni'imarsa gareku da iyalanku.Allah ya sa haka amin.
Ina son in yi amfani da wannan dama, domin in isar da manufofina zuwa gareku, wanda suka shafi 1. Inganta yanayin ilimi, 2.samar da aikin yi domin ya zama madogara ga kowane matashi ko magidanci, 3. samar da dama domin inganta kananan sana'oi ta hanyar bayar da tallafi. 4. Inganta kiwon lafiya.5. Samar da ababen more rayuwa da sauransu.
Ni Abu Najakku, na rantse da Allah cewa Allah daya ne, hakazalika na yi imani cewa shugaba Muhammadu Buhari adilin Dattijo ne mai gaskiya da ke nufin alhairi ga talakkan Najeriya.
Sakamakon haka ya sa na fito domin in yi masa hidima tare da ku jama'armu. Ku bani dama ta hanyar zabena zuwa wannan Majalisar domin in taimaka wajen ganin mun maye gurbin wadanda ke kawo ma shugaba Buhari cikis a cikin zauren Majalisa.
Ta haka kuma za mu ba ku ingantaccen wakilci idan Allah ya lamunta. Jama'ar kasar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza, ina yi maku godiya tare da fatar alhairi da ku da iyalanku gaba daya.
Allah ya taimaki shugaba Muhammadu Buhari, Gwamna Atiku Bagudu, kuma Allah ya bamu nassarar kasancewa dan Majalisa mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza insha Allahu tare da amincewarku. Na gode Allah ya sa mu dace. Amin.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira