Type Here to Get Search Results !

Karanta abin da dan takaran Gwamnan jihar Kebbi Ibrahim Nayelwa ya gaya wa jama'a

Isyaku Garba | 25-8-2018 |

A cigaba da zagaye da yake yi domin sada zumunta tare da isar da sakon gaisuwar Sallah ga jama'ar jihar Kebbi, Alh Ibrahim Aliyu Nayelwa dan takaran kujerar Gwamnan jihar Kebbi, ya isar da sakon zumunta ga jama'ar garin Jega, Bunza, Tilli, Kuka , da Nayelwa ranar Juma'a.

Tawagar dai ta sami kyakkyawar tarbo daga dimbin matasa a garin Jega,  tare da bayar da goyon baya ga Ibrahim Nayelwa. Hakazalika matasan garin Bunza, sun tabbatar da goyon bayansu ga tan takaran.

A dukkannin garuruwa da tawagar dan takaran ta ziyarta, matasa sun tabbatar da goyon baya ga Ibrahim Aliyu Nayelwa. Matasan sun bayar da dalilai kamar rashin cika alkawari daga gwamnati da ke mulki a yanzu ta kin samar da tallafi da ayyukan yi ga matasa.

Matasan sun zargi gwamnati da ke kan gado da tallafa ma zababbun matasa kalilan ba tare da la'akari da sauran kananan hukumomi ba.

Hakazalika matasan sun kalubalanci gwamnati da rashin samar da hanyar mota a garin Nayelwa , sakamakon haka jama'ar Nayelwa na shan wahalar sufuri.

Alh. Ibrahim Nayelwa, ya yi alkawarin samar da ababen more rayuwa, kamar ruwan sha ga al'ummar karkara, samar da tallafi da ayyukan yi ga matasan jihar Kebbi ba tare da nuna bangaranci ba , samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya , ilimi da hanyoyin mota ga al'ummar karkara da kewaye.

A ziyara da dan takaran ya kai ga Sarakunan gargajiya na Kalgo, Bunza, Tilli, Kuka da Nayelwa, Sarakunan sun yi na'am da dan takaran tare da yi masa fatar alhairi. Hakazalika Sarakunan Kalgo da Bunza sun ba dan takaran shawarwari masu amfani.

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN