Gabanin wata ganawa ta karshe da shugabannin tsagin R-APC
zasu yi da shugabancin APC a daren yau, Lahadi, jaridar Tribune ta wallafa wani
rahoto dake kunshe da sakon 'yan tsagin na R-APC.
Rahoton ya bayyana cewar shugabannin R-APC din sun mika wasu
bukatu 7 da suke burin shugaba Buhari ya cika masu a matsayin dama ta karshe da
zasu bawa APC da gwamnatin Buhari kafin su fice cikin sati mai zuwa. Bangarorin
biyu sun amince da yin wata ganawa da zata zama ta karshe a jerin ganawar yin
sulhu da suke ta yi. Ga jerin bukatun kamar yadda jaridar ta Tribune ta
rawaito;
1. Tabbatar da dorewar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar
dattijai bayan zaben 2019.
2. Tabbatar da Yakubu Dogara a matsayin shugaban
majalisar wakilai bayan kammala zaben 2019.
3. Mayarwa da 'yan tsagin R-APC dukkan mukamansu da sabon
zaben shugabannin APC ya tafi da su.
4. A rushe zaben shugabannin jam'iyyar APC
a jihohin da aka samu rabuwar kayuwa yayin zabukan shugabannin jam'iyyar.
5. A
sake yin zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa domin samar da shugabanci mai
karfi.
6. Mayarwa da duk 'yan tsagin R-APC tikitin takara ba tare
da wani sharadi ko zaben fitar da gwani ba.
7. A janye dukkan wata kara da
barazanar shiga kotu da 'yan tsagin R-APC. Wata majiya ta bayyana cewar wani
wakilci daga ofishin shugaban kasa ya gana da Sanata Danjuma Goje tare da yi
masa alkawarin cewar za a sassauta shari'ar da ake yi a kansa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa .naij.ng