Daga karshe dai Bukola Saraki ya fita daga jam'iyar APC


Labarin da ke shigowa yanzu da dumi-dumi na nuna cewa bayan rikice-rikice, zanga-zanga da fadan baki, shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar APC.

Shugaban majalisan ya yi wannan sanarwa ne da yammacin nan ta shafin sada ra'ayi da zumuntarsa na Tuwita. A jawabin yace: " Ina son sanar da yan Najeriya cewa bayan shawarwarin da nayi sosai, na yanke shawaran fita daga jam'iyyar All Progressives Cogress APC." Wannan abi na faruwa ne bayan wasu daruruwan matasa sun tafi zanga-zanga sakatariyan jam'iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja.

An fara samu baraka a jam'iyyar APC ne tun ranar Talatan da ya gabata, 24 ga watan Yuli, 2018 inda yan majalisan dattawa akalla 15 suka fita daga jam'iyyar APC da yan majalisan wakilar 35. Abin mamakin shine Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara da shugaban majalisan, Bukola Saraki, sun zauna a jam'iyyar. Masu sharhi sun bayyana cewa akwai wani kaidi da suke shirin kullawa da wannan rashin fita da sukayi.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN