isyaku.com | 4-7-2018
An yi ma wasu Malaman makarantar sakandare na Malaman Makarantar koyon kimiyya na Waziri Umaru da ke garin Birnin kebbi koran kare daga Makarantar bayan sun amsa cewa suna yin lalata da wata dalibar makarantar 'yar aji 3 a makarantar. kamar yadda Daily Sun ta ruwaito
Bayanai sun ce bayan maganar ta bullo, hukumar Makarantar ta nada wani kwamiti da ya gudanar da bincike a kan lamarin, sakamakon binciken kuma ya nuna cewa Malamai biyar da aka zarge suna yin lalata da yarinyar a lokaci daban-daban.
Sakamakon haka kuma hukumar bayan ta karbi rahotun kwamitin sai ta kori Malaman tare da 'dalibar daga Makarantar.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira