Buhari yace majalisar dokokin tarayya ta zabge kudi 347
billion Naira cikin ayyukan 4,700 da aka gabatar ma ta amma suka sanya ayyukan
kansu guda 6,403 na kimann kudi 578 billion Naira. Kana ya tuhumci yan
majalisar da karawa kansu kudi 14.5 billion ba tare da tuntubar bangaren
zantarwa ba a kan hakan.
Shugaba Buhari yace: "Wan misali shine kasafin kudin
majalisar 14.5 billion. Daga 125 billion zuwa 139.5 billion Naira ba tare wani
tattauwa da fadar shugaban kasa ba. Wani abin takaici shine wani karin da
majalisar tayi na taransfa na kimanin kudi 73.96 billion Naira. Yawancin
kudaden nan na albashi ne a irin wannan lokaci da gwamnati ke kokarin rage
kudin albashin yan siyasa. Duk da haka, zan sanya hannu kan kasafin kudn 2018
saboda kada a kara samun matsala cikin farfadowar tattalin arzikinmu wanda
jinkirin rashin tabbatar da kasafin kudin ya janyo. Bayan haka, ina da niyyar
gyara wannan katobara da sukayi ta hanyar sake aika wani sabon kasafin kudi
kuma ina kayutata zaton majalisa za tayi gaggawar tabbatarwa."
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng