A wani harin da
Amurka ta kai kan gidan shugaban 'yan Taliban bangaren PAkistan, bayan da ta
shafe shekaru gommai tana nemansa ruwa a jallo, tayi nasarar kashe shi yana
shirin fita sallar idi bayan gama azumin watan Ramadana a jiya da safe.
Kafar
yada labaran kasar Pakistan ta tabbatar da harin, inda kuma tashe, harin, ya
kashe iyalinsa mai shekaru 10 da haihuwa, da ma wadansu da basu ji ba basu gani
ba, saboda suna makwabtaka dashi.
Shi dai Mullah Fadhlullah, yayi kaurin suna
wajen kisan mummuke, kan shugabannin siyasar kasar Pakistan, da ma hare-hare
kan yara musamman a makarantun Boko da masu hira a talabijin, kamar dai yadda
yayi wa Malala Yusufzai.
Ya fara shugabantar kungiyar shekaru biyar da suka wuce,
bayan da wani hari makamancin wannan ya hallaka tsohon shugaban Taliban din. Su
dai Taliban, kamar Boko Haram, sun shafe shekaru kusan arbain suna fada da
gwamnati kan kokarin kawar da mulkin Boko da kawo shari'ar Islama ga jama'ar
kasashen Pakistan da ma Aghanistan.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng