• Labaran yau


  Jirgin sama dauke da 'yan wasar kwallon kafa na Saudiya ya kama da wuta a sararin samaniyya

  Jirgin sama dauke da 'yan wasar kwallon kafa na kasar Saudiya ya yi saukar gaggawa bayan gobara ya tashi a cikin jirgin yayin da yake tafiya a sararin samaniyya.

  Yan wasan kwallon kafar kasar ta Saudiya suna kan hanyarsu ce ta buga wasa tsakaninsu da kasar Uraguay ranar Laraba, amma sai aka kula jirgin ya kama da wuta sakamaon haka jirgin ya yi saukar gaggawa a filin saukar jirage na Rastov.

  Wata sanarwa da ta fito daga hukumar kwallon kafa na Saudiya ya tabbatar wa jama'a cewa duk 'yan wasan da jami'an hukumar kwallon kafa na Saudiya da ke cikin jirgin sun sauka lafiya kalau.Haka zalika sanarwar ta ce lamarin ya kasance ne sakamakon wata 'yar matsala da ta taso daga injin na jirgin.

  Kungiyar kwallon kafa ta Saudiya dai ta sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta kasar Rasha bayan Rasha ta lallasa kasar Saudiya da ci 5-0 ranar Alhamis a gasar cin kofin Duniya.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jirgin sama dauke da 'yan wasar kwallon kafa na Saudiya ya kama da wuta a sararin samaniyya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama