Ma'aikatar
Tsaro ta Sudan ta bayyana cewa, wajibi ne ta ci gaba da taya Saudiyya
kai hare-hare a Kasar Yaman wanda hakan wanibangare ne na cika
halayyarta mai kyau.
Sanarwar ta
rawaito ganawar Ministan tsaro na Sudan Ahmad Awad ibn Awf ya yi da
Mataimakin Ministan Tsaron Saudiyya Muhammad Al-Ayash da ya ziyarci
Khartoum inda ya gana da Shugaban Sudan Umar Al-Bashir da kuma Ministan
tsaron kasar.
A ranar 7 ga watan
Afrilu kakakin 'yan ta'addar Houthi 'yan Shi'a ya sanar da cewa, an
kashe sojojin Sudan da dama a garin Midi na yankin Hajjaj da ke Kasar ta
Yaman.
Amma Hukumomin Saudiyya ko na Sudan ba su tabbatar da wannan magana da kakakin 'yan ta'addar ya yi ba.
Tun
shekarar 2014 yaman ta fada yakin basasa bayan da 'yan ta'addar Houthi
suka kwace iko da San'a Babban Birnin Kasar. tare da yunkurin kwace
gwamnati.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI