• Labaran yau


  Kirayen Sanata Melaye, PDP ta bukaci kada yayanta su kada kuri'ar amincewa

  Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta bukaci magoya bayanta kada su kada kuri'ar amincewa da karaye ga Sanata Dino Melaye . Hukumar INEC za ta fara tantance sunayen mutane da suka sa hannu domin  kirayen Sanatan.

  A ranar 28 ga watan Aprilu ne INEC za ta fara tantance sunayen. Wani jawabi da ya fito daga jam'iyar ta PDP a Lokoja na jihar Kogi ya ce tun azil jam'iyar bata goyon bayan wannan kiraye.

  Hukumar INEC ta ce za a fara aikin tantance sunayen daga karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana a Mazabu 552 cikin 560 na kananan hukumomi 7 da suka haifar da Mazamar Sanata na Kogi ta yamma.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kirayen Sanata Melaye, PDP ta bukaci kada yayanta su kada kuri'ar amincewa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama