Kebbi: Yansanda sun kama Fulani da suka yi garkuwa da mutane a Koko-Besse

Yansanda a jihar Kebbi sun kama wasu masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.An kama mutanen guda hudu a karamar hukumar Koko-Besse kuma wadanda aka kama Fulani ne.Haka zalika an gano kudin fansa N800.000 da suka karba a hannun yan'uwan wadanda suka yi garkuwa da su.

Wadanda aka kama sun yi nassarar karbar N300.000 daga Naira miliyan uku da suka bukata daga shugaban Fulani na karamar hukumar Koko-Besse Alh. Aliyu Abubakar Dikko Ardo. Haka zalika sun karbi wasu karin N500.000 daga wani da ba'a tantance sunansa ba kawo yanzu.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi DSP Suleiman Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce rundunar za ta gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.



Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN