• Labaran yau

  Yansanda a kasar Ghana sun kama yan Yahoo 10 yan Najeriya

  Yansanda a Accra  na kasara Ghana sun kama wasu samari guda goma bisa zargin kasancewa yan Yahoo.An kama samarin ne a rukunin gidaje na Ashongman .

  Wadanda aka kama sun hada da  Diamond Andy, 22, Benson Romeo, 20, Randy Samuel, 25, Kelvin Agho, 23, Osas Igbo, 21, David Okondu, 23, Praise Onyekwena, 22, Ohis David, 25, Duru Wisdom, 22 da Uyi Ighodaro, 24.

  An sami modem 34 da Sim daban daban, komputa Laptop 9, wayar salula 5.Yansanda a runduna ta Kwabenya sun yi diran mikiya ne a hotal da aka kama samarin.

  Kwamandan yansanda DCOP George Alex Mensah ya ce an kama samarin ne domin gain yadda suke pacaka da kudi kuma bincike ya nuna cewa basu yin wani aiki.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansanda a kasar Ghana sun kama yan Yahoo 10 yan Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama