• Labaran yau

  Yadda birai suka kwace ragamar wata al'umma a Lagos

  Mazauna unguwar Soluyi-Sosanya a Gbagada na jihar Lagos sun bukaci hukumomi su kawo masu dauki bayan goggon birai sun addabe su a gidajensu kuma suka hana su sakat.

  Shugaban masu gidajen haya na unguwar Mr. Adigun Olaleye ya ce biran sukan fito ne daga wani daji da ke kusa da unguwrar kuma sukan shiga gidaje ba sallama ta hanyar fadowa cikin gidaje da dakunan mutane.

  Ya ce sakamakon haka biran sukan yi barna ta hanyar karya kujeri,da duk wani abin da suka gani a cikin gidaje.

  Daga karshe Mr. Adigun Olaleye ya bukaci hukumomi su taimaka a kori biran ko a kama su.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda birai suka kwace ragamar wata al'umma a Lagos Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama