Karanta yadda wani soja ya kashe dansanda da duka

Wani jami'in dansanda mai suna Imomoh ya mutu bayan wani soja ya noshe shi a wajen bikin bizine gawa a garin Sapele na jihar Delta yan kwanaki da suka wuce.

Rahotanni sun nuna cewa wasu sojoji ne ke harbi da bindiga a cikin iska a lokacin biki bayan sun kwankwadi barasa sai jami'in dansandan wanda baya cikin kaki a lokacin ya je ya roke su cewa su daina harbi a wajen bikin domin kaucewa hadari.

Ganin haka ke da wuya sai daya daga cikin sojan ya harzuka kuma ya kai  wa dansandan duka ta hanyar noshe shi a kirjinsa ba tare da sojan ya san cewa dansanda ne ba.

Bayanai sun nuna cewa dansandan ya yi yunkurin ya rama amma jama'a suka ba shi hakuri, saakamakon haka sai ya bar wurin ,yana cikin tafiya domin ya bar wajen bikin ne sai ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu nan take.

Ganin haka ke da wuya sai sojojin suka tattara nasu da nasu suka gudu suka bar wajen bikin.

Amma wata majiya ta labarta cewa yanzu haka hukumar yansanda a jihar Delta ta fara gudanar da bincike domin kamo wadannan sojoji.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN