• Labaran yau

  An tsinci yara 2 da aka ajiye a bayan wani gida a Zuru

  An tsinci wadansu kananan yara yan kimanin shekara biyu dukaninsu a bayan wani gida a shiyar Unguwar Zuru da misalin karfe biyu na dare ranar Litinin.

  Ana kyautata zaton cewa wata mata ce wacce ba a gane ko wacece ba ta ajiye jariran a bayan gidan ita kuma ta kara gaba.

  Samun labarin ke da wuya shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya umarci sashen kula da jin dadin jama'a na karamar hukumar daukan mataki na gaggawa domin ceton rayukan wadannan yara maza guda biyu.

  Yanzu haka ana gudanar da bincike yayin da shugaban karamar hukumar Zuru ya samar da ababen da suka wajaba tare da ingantaccen tanadi a mataki na farko domin kulawa da yaran.

  Idan baku manta ba, kimanin makonni shida da suka gabata an tsinci wani jariri a unguwar Road Block a garin Zuru wanda tuni shugaban karamar hukumar Zuru ya samar da ababen da suka wajaba domin ceton raywar wannan jariri.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An tsinci yara 2 da aka ajiye a bayan wani gida a Zuru Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });