Ziyarar Mataimakin Gwamnan Kebbi Samaila Yombe a Masarautar Zuru

A karshen mako da ya gabata watau ranar Asabar 24 ga watan Febrairu Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya ziyarci mazabarsa ta Zuru.Daga bisani ya halarci daurin Auren Aina'u Abdullahi wacce aka aurar da ita ga Umar Sani a kan Sadaki N50.000.Mataimakin Gwamna Samaila Yombe ne Uban Amarya a wajen addu'ar daurin auren bisa wakilcin karramawa kuma shi ne ya bayar da auren Aina'u ga Umar.

Addu'ar daurin auren ya sami halarcin daruruwan jama'a daga yankin Zuru da kewaye har da wadanda suka zo daga wajen jihar Kebbi.Imam Hassan na Masallacin Juma'a na Izala1 ne ya daura auren ya kuma roki Allah ya albarkaci auren.Manyan Limamai da Ulama sun sami halartar addu'ar daurin auren.

Haka zalika Manyan Mutane daga kowane fanne na rayuwa sun sami halaratar wannan auddu'ar daurin aure wanda ya hada da Sakataren jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Abubakar Kana, Dan Majalisa mai wakiltar Zuru Hon. Sani Ka'ida, shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Muhammad Kabir Abubakar, shugaban hukumar zabe na jihar Kebbi Alh. Kabiru Yakaji, Alh. Jafaru (clean),Alh.Muhammad Ankwai, Alh. Isah Abdullahi Zuru da sauransu.

Daga bisani Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe, ya saurari kungiyoyin Matasa da yan Siyasa a bisa tsari na cudani domin fahimtar matsalolinsu tare da gabatar da shawarwari a kan yadda za'a ciyar da kasar Zuru gaba.

Bayan haka ,Yombe ya halarci taron wa'azi na kasa da kungiyar Izala ta shirya a garin Ribah tare da tawagarsa .

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN