• Labaran yau


  B-kebbi: Motar tipa ta tsunduma cikin rami sakamakon karancin hanya - Hotuna

  Wata motar tipa wacce ake kyautata zaton ta dauko yashi ne ta tsunduma a cikin wani rami bayan motar ta dawo da baya yayin da ta tsaya domin a jaye wayar wutar lantarki sakamakon haka sai motar ta tsunduma a cikin ramin wanda dalilin haka direban motar mai suna Malam Shu'aibu Lawal ya rasa ransa.

  Ibtila'in ya faru ne da misalin karfe daya na rana gadan Obi a unguwar tsohuwar gidan yari yamma daga gidan Malam Mainassara  motar kiran Mandeisel mai lamba XA 915 BRK ce wanda Malam Shu'aibu ke janye da ita.

  Wata majiya ta shaida mana cewa wannan ba shi ne karo na farko da hakan ya faru a wannan wurin ba, kuma wannan yana faruwa ne sakamakon karancin fadin hanyar.

  Wannan wurin wani katon rami ne kuma majiyar mu ta shaida mana cewa mutanen unguwar ne daga  suka gudanar da aikin gayya domin samar da gadar wacce ta hada al'ummomin yammacin unguwar da bangaren gabacin unguwar a garin Birnin kebbi.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi Suleiman Mustapha ya tabbatar mana da faruwar lamarin inda ya kara da cewa "Direban motar Shu'aibu Lawal ya rasu sakamakon raunuka da ya samu a hadarin ".

  Daga Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: B-kebbi: Motar tipa ta tsunduma cikin rami sakamakon karancin hanya - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama