Yan fashi sun fitar da hanjin direba suka yanke har waje 2

Wani mutum mai suna  Mr George Tayokhe ya rayu duk da yake yan fashi da makami sun tare shi suka yi masa fashi ta hanyar kwace masa dubban kudi da yake dauke da shi bayan sun tare motar tilera da yake tukawa daga bisani suka kai shi cikin daji suka daba masa wuka da ya yi sanadin fitowar hanjinsa daga karshe suka yanke hanjin har waje biyu.

Bayan wani lokaci sai yaron mota wanda ya tsere bayan yan fashin sun tsayar da motar ya je ya kira wadansu sojoji da ke sintiri kimanin kilomita biyu daga wajen da lamarin ya faru a jihar Enugu . Sojojin ne suka kai shi Asibiti inda aka dinke hanjin.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN