• Labaran yau


  Gwamnatin jihar Kebbi ta sa hannu a kasafin kudi N151.2b na 2018

  Gwamanatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ta rattaba hannu a kasafin kudin 2018 na Naira Biliyan 151.2 bayan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi ta amince da kasafin da aka gabatar mata a karshen watan Disamba na 2017.

  Gwamna Bagudu ya rattaba hannu a dokar kasafin kudin na 2018 a wani takaitaccen biki da aka gudanar a dakin taro na gidan Gwamnatin jihar Kebbi a garin Birnin kebbi ranar Juma'a

  Gwamna Bagudu ya ce Gwamnati za ta kashe Naira biliyan dari da takwas (N108b) a manyan ayyuka a fadin jihar Kebbi yayin da Naira biliyan arba'in da biyu da digo tara (N42.9b) za'a kashe a ayyukan yau da kullum da sauran kananan ayyuka.

  Wadanda suka halarci bikin sun hada da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai, Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kebbi Alh. Abdulmuminu Samaila Kamba, tare da Mataimakinsa Muhammadu Buhari Aliero, shugaban masu rinjaye na Majalisa Alh. Bello Yakubu Rilisco da sauran 'yan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi.

  Saura sun hada da Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Alh. Babale Umar, Shugaban Ma'aikata na jihar Kebbi Alh.Udu ,Kwamishinoni , Mai Martaba Sarkin Gwandu Alh. Iliyasu Bashar, Shugaban jam'iayar APC na jihar Kebbi Barr. Attahiru Maccido, Sakatarorin dindindim, shugabannin kananan hukumomi tare da manyan jami'an Gwamnatin jihar Kebbi.

  Daga Isyaku Garba a Birnin kebbi


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnatin jihar Kebbi ta sa hannu a kasafin kudi N151.2b na 2018 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama