Sojan bogi ya gurfana a gaban Kotu bisa zamba da cin amana

Wata Kotun Majistare a garin Osogbo a jihar Osun ta garkame wani matashi mai shekara 32 a Kurkuku bayan ya yi sojan gona, wanda aka kama mai suna Abu Jonah ya gabatar da kan shi ne a matsayin Leutenant na sojin Najeriya.

Mai gabatar da kara Oladoye Joshua ya gaya wa Kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a 2016 da 9 ga watan Janairu 2018.

Joshua ya ce an kama wanda ake zargi da tufafin soji, takalman soji da takardar shaidan aikin soja na bogi.

Mai gabatar da karan ya ce ana zargin cewa Jonah ya karbi N180.000 a hannun wani Abdulwaheed Yusuf, N100.000 daga hannun Aduragbemi Adebowale, N32.000 daga hannun Jegede Aderemi da N19.000 a hannun Solere Oluwaseun. Wanda ake zargin ya karbi kudaden ne da niyyar cewa zai sama wa mutanen aiki a NSCDC amma ya kasa.

Alkalin Kotun bai karbi koken wanda ake zargi ba ya kuma bayar da umurni cewa a kai wanda ake tuhumar a gidan Kurkuku har sai zaman Kotun na gaba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN