Rundunar Sojin Najeriya ta musanta sanin inda Shakau ya tsere

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya tsere zuwa kasar Kamaru.

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce sojin Najeriya basu da masaniya kan inda Shekau ya ke, sabanin yadda wasu rahotanni suka ce, wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram da suka kama, a ranar 14 ga watan Fabarairu, ya shaida musu cewar Shekau ya tsere zuwa Kamaru, hasalima basa tsare da kwamandan da aka kira da Abu Zainab.

A karshen makonnan ne rundunar sojin Najeriya, ta yi shelar bada kyautar naira miliyan 3, ga duk wanda ya taimaka da bayanai wajen gano maboyar jagoran kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau.

A farkon makon watan Fabarairu, jagoran kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon sako na bidiyo, in da yake cewa ya gaji da masifar da suke fuskanta kuma ya gwammace mutuwarsa don hanzarta shiga aljanna.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Daga rfi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN