Kalli korarren dansanda da aka kama yana sojan gona wai shi jami'in EFCC ne

Jami'an hukumar EFCC a birnin Port Harcourt su cafke wani korarren kurtun dansanda mai suna David Lohbut Nimdul wanda ke sojan gona cewa shi jami'in EFCC ne kuma ya zambatar mutane ta hanyar karban kudi.

Wani mutum ne ya rubuta takardar koke kan lamarin Nimdul bayan ya fahimci cewa akwai rashin gaskiya cikin lamurransa.

Bayanin mai koken sun nuna cewa wata ma'aikaciyar Banki ta ari N15,300,000,00 daga wurinsa da alkawarin cewa za ta biya kidin a cikin kwana 120 amma sai ta saba kuma kudin suka makale, sakamakon haka aka hada shi da Nimdul cewa shi jami'in EFCC ne.

Daga isani Nimdul ya je wajen ma'aikaciyar Bankin ya dauki jawabin ta kuma daga bisani ya bukaci ta biya N250,000 a cikin asusun ajiyarsa na Banki wai zai saka kudin a cikin asusun kudaden bashi da ake karba na EFCC amma sai ya lakume kudin .

Bisa wannan jawaabi atakardar mai koke ne sai jami'an EFCC na gaske suka zakulo tare da damke Nimdul kafin bayaai suka fito cewa ai dama a kore shi daga aikin dansanda bayan an same shi da laifin cin amana da sauran ayyukan da suka saba wa kai'dar aikin dansanda.

Nimdul tssohon jami'in Mopol ne wanda ya taba aiki a ofishin EFCC kafin a kore shi daga aikin dansanda.Bayanai sun nuna cewa an kammala bincike akan lamarin Nimdul kuma za a gurfanar da shi a gaban Kotu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN