Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya shawarci uwayen yara cewa su dinga sa yaransu a Makaranta domin sama masu ginshikin ingantaccen rayuwa. Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyara a Makarantar Pramare na Mungadi Sani Nursery and Primary School da Dunbegu Government Day Secondary School a karamar hukumar Maiyama.
Gwamna Bagudu ya nuna rashin jindadi sakamakon rashin gamsuwa da adadin yawan yara da ke makaranta, sakamakon haka ya gargadi Hakimai da Uwaye akan su sa ido domin ganin yaransu sun je Makaranta akan lokaci tare da tabbatar cewa akwai Malamai a Makarantu.
Gwamna Abubakar Bagudu ya tabbatar cewa Gwamnatinsa za ta gyara tare da gina Makarantu da suka lalace, haka zalika ya ce Gwamnati za ta sama wa dalibai kayan jin dadin rayuwa don tabbatar da kwazo a karatu haka kuma Gwamnati za ta kara inganta jin dadin Malamai a fadin jihar Kebbi.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com